rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Vatican Bolivia Paraguay Ecuador

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Paparoma na ziyara a kasashen yankin Kudancin Amurka

media
Paparoma Francis na daya kenan, yana gabatar da huduba

Shugaban mabiyar cocin Katolika a duniya Paparoma Francis na daya, ya fara ziyarar aiki a kasashen Kudancin Amurka a wannan lahadi, shekaru biyu bayan zaben sa akan wannan mukami.


Paparoma dai zai ziyarci kasashen Ecuador, Bolivia da kuma Paraguay, to sai Francis ba zai ziyarci kasarsa ta asali ba wato Argentina a wannan karo.

A shekarar da ta gabata shugaban cocin na katolika ya ziyarci kasar Brazil inda ya jagoranci wasu addu’o’i da mutane kusan milyan uku suka halarta a gabar ruwan Copa,cabana da ke birnin Rio de Janeiro.