Britania
'Yan uwan Osama sun rasu a hatsarin Jirgi
A wani sanarwa da suka fitar Ofishin jakadancin kasar Saudi Arabia dake birnin London sun tabbatar da mutuwar dangin marigayi shugaban kungiyar al-Qaeda, Osama bin Laden a wani hatsarin jirgin sama da ya auku a kudancin Ingila.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Talla
Tuni dai Ofishin Jakadancin ta mika ta'aziyarta a hatsarin da aka tabbatar, ya auku a jiya Juma'a.
Jami’an 'Yan sanda yankin sun ce mutane hudu da suka hada da matukin jirgin ne ke cikin karamin jirgin mai lambar kasar Saudia, lokacin da ya rikito kana ya kuma kama da wuta ba tare da ko mutum guda ya tsira ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu