rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Bakin-haure Syria Girka Italiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Facebook da Whatapps na taimakawa ‘Yan ci-rani shiga Turai

media
Daruruwan 'Yan ci-rani ne da ke kokarin shiga Turai suka mutu a teku REUTERS/Alkis Konstantinidis

Dandalayen Facebook da Whatapps a wayoyin Salula na taimakawa ‘Yan ci-rani wajen musayar bayanai a tsakaninsu kan dubaru da kuma yadda za su yi mu’amula da masu sana’ar fataucinsu zuwa kasashen Turai.


Wayar Salula na da matukar muhimmaci ga ‘Yan ci-ranin, domin wasunsu sun ce ta fi abinci muhimmaci gare su.

‘Yan ci-ranin dai na amfani da facebook da Whatapps a tsakaninsu domin taimakon juna ta hanyar musayar bayanai da hotuna da taswirar shiga kasashen Turai.

Sannan suna amfani da hanyar sadarwa ta Viber domin sanar da danginsu cewa sun isa lafiya.

‘Yan ci-ranin dai na ratsa tekun Mediterranean ne su shiga Italiya da Girka kusan a kullum duk da hatsarin mutuwar mutane da ake samu.

A bana sama da ‘yan ci-rani 135,000 aka bayyana sun tsallaka zuwa Girka yawancinsu daga Syria.

Hukumar Turai ta bayyana kwararar ‘Yan ci-ranin a matsayin mafi girma, tun yakin duniya na biyu.