rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Guatemala Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaban Kasar Guatemala ya yi murabus

media
Shugaban Kasar Guatemala mai murabus Otto Perez. REUTERS/Jorge Dan Lopez

Shugaban Kasar Guatemala Otto Perez ya yi murabus daga mukaminsa a yau Alhamis bayan an baiwa jami’an tsaro sammacin kama shi sakamakon zarginsa da hannu dumu dumu a wani kazamin laifin cin hanici da rashawa.


Shugaban wanda ya dare kan karagar mulki a shekarar 2012 ya yanke shawarar yin murabus ne domin fuskantar tuhuma game da zarge zargen da ake masa kamar yadda mai Magana da yawun sa Jorge Ortega ya sanar.

A ranar talata ne majalisar kasar ta cire rigar kayriya ga Perez, lamarin da zai bada damar a gurfanar dashi a gaban kotu.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da ake shirin gudanar da zaben shugabancin Kasar kuma Yanzu haka mataimakinsa Alejandro Maldonado ne zai karbi ragamar shugabancin Kasar har zuwa lokacin da za’a rantsar da sabon shugaban Kasar da zai lashe zabe.

A ‘yan kwanakin nan dai mutane 14 ne daga cikin ministocinsa suka yi murabus tare da wasu manyan jami’an gwamanati kuma a yau ne ake sa ran Perez zai bayyana a gaban Kotu.