rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Guatemala

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Dan wasan barkwanci na kan gaba a zaben kasar Guatemala

media
Dan takarar shugabancin kasar Guatemala Jimmy Morales REUTERS/Jose Cabezas

Dan wasan barkwancin nan mai suna Jimmy Morales ne ke kan gaba a yawan kuri’un da aka kirga zuwa yanzu, a zaben shugaban kasar Guatemala da aka gudanar a jiya Lahadi, bayan cecekucen da aka yi yayin yakin neman zaben, dake zuwa bayan daure tsohon shugaban kasar da aka samu da laifin cin hanci.


Zuwa yanzu dai an kirga fiye da kashi 60 cikin 100 na kuri’un da aka kada, kuma dan wasa Morales mai shekaru 46 a duniya, da ya shahara saboda wasannin da yake fitowa a matsayin sakarai, na kan gaba da kashi 27 cikin 100.
Manuel Baldizon daya dade yana takarar shugabancin kasar a jami’iyyar ‘yan mazan jiya, yana da kashi 18, inda suke kan kan kan da mai dakin tsohon shugaban kasa Sandra Torres, dake da kashi 17 cikin 100.
Da alama babu dan takaran da zai iya samun kashi 50 cikin 100 na kuri’an da aka kada, don kaucewa zagaye na 2 na zaben, don haka akwai yuwuwar komawa rumfunan zabe a ranar 25 ga watan Oktoba mai zuwa, don kece raini tsakanin Morales, da kuma daya daga cikin sauran ‘yan takara 2, da zai zo na biyu a wannan zagayen.
Abinda yafi daukar hankulan mutane yayin zaben shine yadda aka yi ta zanga zanga a kasar, don nuna adawa da cin hanci, da yayin sanadiyyar daure tsohon shugaba Otto Perez.
An sami fitowar kashi 68 zuwa 70 cikin 100 na masu kada kuri’a, a zaben kasar ta Guatemala mai fama da talauci, dake yankin tsakiyar Amurka.
Sakamakon, da ya nuna yadda sabon hannu ke kokarin kayar da tsofaffin hannu, kuma alamace dace nuna al’ummar Guatemala ke bayyana matukar fushi da halaiyyar ‘yan siyasan kasar, lamarin da Morales ya tabbatar a jawabinsa.