Za a biya fursunonin siyasa diyya a Chile
Kotun Kolin kasar Chile ta umurci gwamnatin kasar ta biya diyyar sama da Dala miliyan shida da rabi ga mutane 31 da aka tsare su saboda tirsasawar siyasa a karkashin gwamnatin kama-karya ta Augusto Pinochet.
Wallafawa ranar:
Kotun tace ta gamsu da shaidun da aka gabatar ma ta na cin zarafin da aka yi wa fursinonin siyasar lokacin da ake tsare da su a tsibirin Dawson.
Kotun ta yi watsi da bukatar gwamnatin kasar na watsi da karar inda ta bukaci a biya mutanen 31 makudan kudade saboda halin da aka jefa su iyalansu a ciki.
Fursunonin dai sun kunshi jiga-jigan ‘Yan siyasa da Ministoci gwamnatin gurguzu ta Salvador Allende wanda Pinochet ya yi juyin mulki a 1973.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu