Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka za ta datse tallafinta ga Falasdinawa

Kasar Amurka za ta datse tallafin tattalin arziki da ta ke ba gwamnatin Falasdinawa saboda rikicin masallacin al Aqsa tsakaninsu da Isra’ila, kamar yadda Wata majiyar Diflomasiyar kasar ta bayyana.

Sakataren Harakokin wajen Amurka John Kerry tare da Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas
Sakataren Harakokin wajen Amurka John Kerry tare da Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas REUTERS/Carlo Allegri
Talla

Rahotanni sun ce Amurka za ta datse tallafin da ta ke ba Gaza da Yamma da Kogin Jordan daga dala Miliyan 370 zuwa dala Miliyan 290.

Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry a ziyarar da ya kai a Amman ya tabbatar da matakin datse tallafin ga Falasdinawa.

Kerry kuma yace Amurka da Isra’ila sun amince da daukar wasu matakai na kawo karshen rikici a masallacin Al Aqsa da ke birnin Kudus inda ake rikici tsakanin Yahudawa da Falasdinawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.