wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa
Dan wasan barkwanci ya lashe zaben Guatemala
Al’ummar Kasar Guatemala ta zabi Jimmy Morales dan wasan barkwanci a matsayin shugaban kasar, bayan zargin cin hanci da rashawa ya kawar da shugaban kasar Otto Perez da mataimakinsa daga karagar mulki, wadanda yanzu haka ake tsare da su.
Morales ya samu kashi 69 na kuri’un da aka kada yayin da abokiyar takararsa, kuma matar tsohon shugaban kasar Sandra Torres ta amsa shan kaye bayan ta samu kasha 39.
Masu gabatar da kara da Majalisar Dinkin Duniya sun ce tsohon shugaban da mataimakinsa sun karbi cin hancin da ya kai Dala miliyan kusan 4 a karkasin hukumar kwastam.