Isa ga babban shafi
Rasha

Babu sheda da ke tabbatar da kakkabo jirgin Rasha aka yi

Hukumar leken asiri ta Amurka ta ce babu wata shaida da ke tabbatar da aikin ta’addanci ne ya yi sanadiyar faduwar jirgin fasinjan Rasha a kasar Masar, duk da ikirarin da kungiyar IS ta yi na kakkabo jirgin.

Jami'an tsaro na binciken tarkacen Jirgin Fasinja na Rasha da ta tarwatse a yankin Hassana, arewacin Masar a ranar Assabar
Jami'an tsaro na binciken tarkacen Jirgin Fasinja na Rasha da ta tarwatse a yankin Hassana, arewacin Masar a ranar Assabar REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Talla

A cewar Daraktan hukumar leken asirin ta Amurka James Clapper, babu wata shaida a zahiri da za a iya amfani da ita har a dora laifin hatsarin jirgin kan aikin ta’addanci.

A jawabin da ya gabatar a wani taron tsaro da aka gudanar a birnin Washington na Amurka, Clapper ya yi watsi da ikirarin ISIS yana mai cewa kungiyar ba ta da karfin da za ta iya amfani da shi har ta kaddamar da irin wannnan farmakin kan jirgin, amma ya ce ba zai yanke hukunci kai tsaye ba.

Shugaban Masar Abdel Fatah al Sisi ya yi watsi da ikirarin mayakan IS da ke da’awar jihadi da suka ce su suka kakkabo jirgin Rasha.

Mahukuntan Rasha da Masar sun yi watsi da ikirarin kungiyar na cewa ita ta haifar da faduwar jirgin wanda ya taso daga Sharm el-Sheik na Masar da nufin zuwa St. Petersburg da ke Rasha amma ya gamu da hatsari dauke da mutane 224 a cikinsa kuma babu wanda ya tsira da rai.

A bangare guda, hukumomin jirgin na Rasha sun bayyana cewa wasu dalilai ne can na waje suka haifar da wannan hatsarin yayin da iyalan mamatan suka fara gane gawarwakin ‘yan uwansu bayan an isar da su zuwa birnin St. Petersburg na Rasha a jiya Litinin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.