rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
Gaggauce
Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Ganduje a matsayin gwamnan Kano

Ingila David Cameron ISIL Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sunan ISIS ya koma Daesh

media
Majalisar Britaniya na Muhawara kan fara kaiwa IS hare-hare REUTERS

Firamnistan Birtaniya David Cameron ya amince da Daesh a matsayin sabon sunan mayakan IS masu da’awar jihadi a duniya. Firaministan ya amince da sabon suna ne a yau Laraba a gaban ‘Yan Majalisun kasar da ke muhara kan amincewa da matakin fara kai wa mayakan hare hare da jiragen yaki.


Daesh dai yanzu ya kasance sabon sunan da ake kiran mayakn IS da shi, kuma a yau Laraba ne Firaministan Birtaniya David Cameron ya amince da sabon sunan sabanin ISIL ko ISIS.

Tuni dai shugaban Faransa Francios Hollande ke kiran mayakan da sunan Daesh.

Daesh dai larabci ne aka takaita da ke nufin al-daular islamiya fil iraq wa al-sham.
Wato daular musulunci a Iraq da Syria.

Wasu rahotanni sun ce mayakan na IS basu son a kira su da sabon sunan.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da ‘yan majalisar Birtaniya ke muhara kan amincewa da matakin fara kai hare hare da jiragen yaki a kan mayakan IS.