Isa ga babban shafi
Asia

Interpol ta kame jabun Magani a Asia

Rundiyar ‘Yan Sandan duniya da ake kira Interpol ta sanar da kwace jebun magungunan da kudinsu ya kai Dala miliyan 7 a cikin kasashe 13 na Yankin Asia.

Tambarin hukumar 'Yan sandan kasa da kasa
Tambarin hukumar 'Yan sandan kasa da kasa
Talla

Aline Plancon, shugaban sashen kula da magunguna yace sun kunshi na hawan jini da rigakafin cizon Kare da kuma rigakafin cututtuka, sannan sun kama mutane 87.

Kasashen da kamen ya shafa sun hada da Afghanistan da Cambodia da China da India da Indonesia.

Sauran sun hada da Laos da Malaysia da Myanmar da Pakistan da Philippines da Singapore da Thailand da kuma Vietnam.

Hukumar lafiya ta MajalisarDinkin Duniya ta bayyana cewar matsalar tafi kamari a Asia da Amurka ta kudu da kuma Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.