Isa ga babban shafi
Iran

An janye wa Iran takunkuman tatttalin arziki

Kungiyar tarayyar Turai ta bayyana cewa an janye takunkuman da aka kakaba wa Iran akan shirinta na Nukliya bayan gwamnatin kasar ta aiwatar da yarjejeniyar da ta cimma da manyan kasashen duniya a ranar 14 ga watan Yulin bara.

A ranar 14 ga watan Yulin bara Iran ta cimma yarjejeniya da manyan kasashen duniya 6 kan shirinta na Nukliya a birnin Vienna na kasar Austria
A ranar 14 ga watan Yulin bara Iran ta cimma yarjejeniya da manyan kasashen duniya 6 kan shirinta na Nukliya a birnin Vienna na kasar Austria REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Shugabar harkokokin wajen kungiyar tarayyar Turai ce, wadda kuma ta wakilci manyan kasashen, Federica Mogherini ta sanar da haka a jiya Asabar a birnin Vienna na kasar Austria.

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya yaba da matakin, inda ya ce hakan babbar nasara ce ga kasarsa.

Tuni dai Majalisar dinkin duniya da wasu kasashen da suka hada da Faransa da Birtaniya suka yi marhaba da matakin yayin da wasu kuwa ke yin tur da shi.

Wannan dai na zuwa ne bayan hukumar da ke sa ido kan makamashin Nukliya ta duniya, IAEA ta tabbatar cewa Iran ta cika sharuddan da aka gindaya mata dangane da mallakar makamin Nukliyan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.