Isa ga babban shafi
Switzerland

Kasashen duniya na taron tattalin arziki a Davos

Shugabannin kasashen duniya da manyan ‘yan kasuwa da masana tattalin arziki da kwararru a fannin kimiya da fasaha na gudanar da taron tattalin arziki a birnin Davos na kasar Switzerland, inda za su tattauna kan batutuwa da dama da suka hada da kasuwanci, ta’addanci, fasaha da matsalar kwararar ‘yan gudun hijira. 

Taron tattalin arziki na wannan shekarar a Davos na Switzerland
Taron tattalin arziki na wannan shekarar a Davos na Switzerland REUTERS/Ruben Sprich
Talla

A yammacin jiya talata ne aka bude taron wanda za a shafe kwanaki hudu ana gudanar da shi kuma taken taron na bana shi ne, kwarewa wajan ci gaban masana’antu.

Taron zai tattauna akan kalubalen da ake fama da shi dangane da tattalin arzikin duniya tare da mayar da hankali akan kasuwannin hannayen jari da ke cikin wani hali a yanzu.

Hakazalika taron zai tattauna game da matsalar rashin aikin yi tare duba barazanar da miliyoyin ma’aikata ke fuskanta.

Shuagabbnin duniya da hukumomin agaji dabam dabam za su tafka muhawara kan matsalar kwararar ‘yan gudun hijira da kuma yadda za a samar musu da matsugunnai yayin da ake sa ran sarauniya Rania ta Jordan za ta gabatar da jawabi kan dalilan da ke tirsasa wa miliyoyin mazauna yankin gabas ta tsakiya yin kaura zuwa Turai.

A bangare guda, shugabannin za su zanta kan matsalar ta’addanci wadda ta zama ruwan dare a sassan duniya.

Sauyin yanayi na daya daga cikin manyan matsalolin da taron zai yi magana a kai , sannan zai karfafa yarjejeniyar da duniya ta cimma a birnin Paris a karshen shekarar da ta gabata dangane da matsalar dimamar yanayi.

Baya ga wadannan akwai sauran batuwawa da taron zai zanta a kan su kamar matsalar kutse ta yanar gizo da kuma kiwon lafiya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.