Isa ga babban shafi
Twitter

Twitter ya dakatar da mutane dubu 125 saboda ta'addanci

Dandalin sada zumunta na Twaitter ya dakatar da masu amfani da shi har 125,000 akasarinsu masu alaka kungiyar IS mai dawa’ar jihadi, a wani mataki na kawar da sakwannin ta’addanci da ake aika wa ta dandalin.

Twitter ya dakatar da masu amfani da shi 125,000 saboda ta'addanci
Twitter ya dakatar da masu amfani da shi 125,000 saboda ta'addanci © AFP
Talla

Twaitter ya bayyana a shafinsa na dokoki cewa, ya damu matuka da ta’asar da kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi ke yi.

Sannan ya yi alla-wadai kan yadda ake amfamni da shi wajen dabbaka ayyukan ta’addanci a duniya.

Daukan matakin dai na zuwa ne bayan Amurka da gwamnatocin wasu kasashen sun bukaci shafukan sada zumunta da su kara kaimi wajen dakile yunkurin shirya miyagun ayyuka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.