Isa ga babban shafi
Malaysia- Australia

Dangi da 'Yan Uwan Wani Fasinja dake cikin Jirgin Malaysia MH370 Sun Shigar da Kara Kotu

Dangi  da ‘yan uwa na wani fasinja dake cikin jirgin saman shekaru biyu da suka wuce,  kuma ake ganin mutane 239 dake cikin jirgin sun mutu ne  ya shigar da kamfanin jirgin na Malaysia kotu saboda neman abi masu hakkin firgici da tsoro da yake ciki tun rasa dan uwansu da suka yi.

Daya daga cikin dangi na mamata dake cikin jirgin sama na Malaysia Airline ta na kuka a bukin cika shekaru biyu da bacewar jirgin
Daya daga cikin dangi na mamata dake cikin jirgin sama na Malaysia Airline ta na kuka a bukin cika shekaru biyu da bacewar jirgin REUTERS/Kim Kyung-hoon TPX IMAGES OF THE DAY
Talla

Dangi da ‘yan uwa na mutumin mai suna Paul Weeks dake cikin jirgin fasinjan na neman a dauki mataki ne gameda kamfanin jiragen saman na Malaysia wanda ya mallaki jirgin.

Sun shigar da kara ne gaban kotu dake Yammacin Australia.

A ranar 8 Maris 2014 jirgin saman fasinja na Malaysia, MH370 ya bace bayan ya tashi daga Kuala Lumpur zuwa Beijing na kasar China.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.