Isa ga babban shafi
Turkiya

Turkiya na tilasta wa 'yan gudun hijira komawa Syria

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bayyana cewa, kasar Turkiya na tilasta wa dubban ‘yan gudun hijirar Syria komawa kasarsu ta asali, a dai dai lokacin da ake sa ran za ta fara karbar gungun ‘yan gudun hijira daga Girka. 

Amnesty ta ce, Turkiya na tilasta wa 'yan gudun hijirar Syria komawa kasarsu ta asali
Amnesty ta ce, Turkiya na tilasta wa 'yan gudun hijirar Syria komawa kasarsu ta asali 路透社
Talla

Amnesty Intrenational ta ce, a kowacce rana Turkiya na mayar da ‘yan gudun hijira 100 zuwa syria bayan sun guje wa rikicin da ya hana su zama a kasar.

Tun a tsakiyar watan Janairun da ya gabata, Turkiya ta fara mayar da ‘yan gudun hijrar da suka hada da kananan yara da mata, abinda Amnesty ta ce ya saba wa dokokin kasa da kasa.

Kungiyar ta kara da cewa, rahoton da ta fitar ya bayyana kura-kuren da ke tattare da yarjejeniyar da Turkiya ta cimma da kungiyar tarayyar Turai a kwanan-nan wadda aka kulla da nufin dakile yawan bakin da ke kwarara kasar Girka.

To sai dai a nata bangaren, Turkiya ta musanta batun tilasta wa duk wani dan gudun hijira komawa kasarsa ta asali ba tare da son ransa ba.

Rahoton dai na Amnesty na zuwa ne, kwanaki kalilan da ake sa ran Turkiyar za ta fara karban tawagar farko ta ‘yan gudun hijira daga Girka kamar yadda aka shata a yarjejniyar da ta cimma da tarayyar Turai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.