rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Ecuador

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An tabbatar da mutuwar mutane 413 a Ecuador

media
Birnin Pedernales, daya daga cikin biranen da girgizar kasar ta fi yi wa illa RODRIGO BUENDIA / AFP

Gwamnatin Ecuador ta tabbatar da mutuwar mutane 413 sakamakon girgizar kasa da ta afaka wa kasar a karshen mako, yayin da kimanin dubu 2 da 500 suka samu raunuka.


Girgizar kasar mai karfin maki 7.8 ta faru ne a ranar Asabar din da ta gabata yayin da jami’an agaji ke ci gaba da aikin ceto.

A lokacin da ya kai ziyara a yankin da ibtila'in ya shafa, shugaban kasar Rafael Correa ya bayyana cewa aikin sake gina inda lamarin ya faru zai lakume biliyoyin dala.

Correa ya ce, wannnn musibar ita ce mafi muni da Ecuador ta gamu da ita a cikin shekaru 70 da suka gabata.

An dai gudanar da  jana’izar wasu daga cikin mamatan da girgizar kasar ta kashe a biranen Portoviejo da Pedernales, inda abin ya fi kamari.