Isa ga babban shafi
us-vietnam

Amurka ta kulla yarjejeniya da Vietnam

Shugaban Amurka Barack Obama da ke ziyara a Vietnam, ya yaba da dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, yayin da suka kulla yarjejeniyar kasuwanci ta Dala biliyan 11. 3, inda Amurkan za ta siyar wa Vietnam jiragen fasinja guda 100 kirar Boeing.

Shugaban Amurka Barack  Obama da takwaransa na Vietnam  Tran Dai Quang a birnin Hanoi.
Shugaban Amurka Barack Obama da takwaransa na Vietnam Tran Dai Quang a birnin Hanoi. AFP
Talla

A yammacin jiya Lahadi ne, Obama ya isa kasar ta Vietnam kuma a yayin ganawarsa da takwaransa Tran Dai Quang a birnin Hanoi, Obama ya ce, mun kawo wannan ziyarar ce domin nuna karfin dangantakar da muka kulla shekaru da dama.

Obama ya kara da cewa, kasashen biyu sun inganta hulda a tsakaninsu domin kowannen su ya amfana.

Wannan ziyara dai za ta kai shi kasar Japan amma ya ce, ba zai bai wa kasar hakuri ba akan makami mai guba da Amurka yi amfani da shi a Hiroshima, yayin da zai kasance shugaban Amurka na farko mai ci da zai ziyarci birnin Hiroshima.

Kalaman Obama sun nuna matsayin gwamnatinsa karara kan batun na Hiroshima wanda ya haifar da tayar da jijiyoyin wuya a Amurkan tare da daukan tsawon shekaru ana tafka muhawara akai.

A ranar 6 ga watan Agustan shekarar 1945 ne, rundunar sojin saman Amurka ta yi amfani da makami mai guba a Hiroshima a lokacin yakin duniya na biyu, abinda ya yi sanadiyar mutuwar mutane dubu 140, kuma a karon farko kenan a tarihin duniya da aka yi amfani da irin wannan makamakin wajen kaddamar da hari kan wata kasa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.