Isa ga babban shafi
Turkiya-Israel

Isra'ila za ta biya Turkiya diyyar dala miliyan 20

Kasar Isra’ila ta amince ta biya Turkiya dala milyan 20 a matsayin diyya saboda kisan da jami’anta suka yi wa Turkawa 10 a shekara ta 2010 a zirin Gaza, abinda ya haifar tsamin danganta tsakanin kasashen biyu.

Firaministan Turkiya Binali Yildirim ya sanar da dinke barakar da ke tsakanin kasashen biyu
Firaministan Turkiya Binali Yildirim ya sanar da dinke barakar da ke tsakanin kasashen biyu REUTERS/Umit Bektas
Talla

Firaministan Turkiya Binali Yildrim ya sanar da haka a yau litinin yayin da takwaransa na Isra’ila Benjamin Netanyanhu y ace, wannan wani mataki ne da zai habbaka tattalin arzikin kasarsa.

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya yi fatan cewa, matakin zai inganta rayuwar al’ummar Gaza da ke cikin wani hali.

Yarjejniyar wadda bangarorin biyu za su sanya wa hannnu a gobe Talata, za ta bai wa Turkiya damar isar da kayayyakin jin- kai ga Falasdinawa tare da samar musu da abubuwan more rayuwa.

A ranar 31 ga watan Mayun shekara ta 2010 ne, jami’an Isra’ila da suka kware wajen kai farmaki suka far wa wani jirgin ruwan Turkiya a Gaza, inda suka kashe mutane 10 masu fafutukar kare hakkin dan Adam.

Sai dai kasashen biyu sun zargi juna da haifar ta rikicin na wancan lokacin, inda Turkiya ta ce, jami’an Isra’ilan ne suka fara bude wuta jim kadan da dirarsu cikin jirgin.

Ita kuma Isra’ila cewa ta yi, jami’anta sun bude wutar ne bayan da aka fara kai musu hari da wukake da kuma bindigar da aka kwace daga hannunsu.

Gabanin samun sabanin, kasashen biyu nada kyakkyawar alaka.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.