Isa ga babban shafi
G20

Gargadin G20 kan illar da ficewar Birtaniya za ta yi

Ministocin kudi na kasashe masu karfin tattalin arziki sun yi gargadi kan irin halin kuncin da duniya za ta tsinci kanta a ciki saboda ficewar Birtaniya daga kungiyar tarayyar Turai.

Kasashen G20 na taro a China, inda suka gargadi halin kuncin da duniya za ta shiga  ta tabarbarewar tattalin arziki saboda ficewar Birtaniya daga Turai
Kasashen G20 na taro a China, inda suka gargadi halin kuncin da duniya za ta shiga ta tabarbarewar tattalin arziki saboda ficewar Birtaniya daga Turai REUTERS/Aly Song
Talla

Gargadin na zuwa ne a yayin da Ministocin ke taro a kasar China a yau Lahadi.

Watanni uku kenan da wakilan gwamnatocin kasashen duniya 20 masu karfin tattalin arziki da kuma shugabannin manyan bankuna, suka bayyana ficewar Birtaniya a matsayin daya daga cikin abubuwan da ke baraza ga tattalin arzikin duniya.

A watan jiya ne, al'ummar Birtaniya suka kada kuri'ar ficewa daga Turai, abinda ya sa tsohon Firaministan kasar, David Cameron ya yi muraabus daga mukaminsa yayin da Theresa May ta gaje shi.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.