Jirgin Fasinja ya fara tashi daga Amurka zuwa Cuba
Jirgin fasinja na farko ya tashi daga Amurka zuwa Cuba, matakin da ke kara tabbatar alaka a tsakanin kasashen biyu da suka jima suna zaman doya da man-ja a siyasance a tsawon shekaru sama da 50.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Jirgin Fasinjan na farko ya sauka ne a garin Santa Clara na Cuba da misalin karfe 11 na safe agogon kasar wanda ya fito daga kudu maso gabashin Florida dauke da fasinja 150.
An yi bikin tashin jirgin a lokacin da zai tashi da kuma sauka a kasashen biyu.
Jirgin dai shi ne na farko cikin jiragen fasinja 110 da ake hasashen za su ci gaba da jigila tsakanin Cuba da Amurka.
Kasashen biyu sun shafe shekaru sama da 50 suna gaba tsakaninsu tun 1958 da aka kawo karshen yakin cacar-baka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu