An bude taron G20 a Chana
A yau ne aka bude taron shekara na kasashen da suka fi habbakar tattalin arzikin duniya da ake kira G20 a Chana inda shugaban Kasar Xi Jingpin ya bukaci shugabanin kasashen dasu kauce yin alkawarin baki wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Yayin jawabi a wajen taron da akeyi a kasar China, shugaba Jingpin ya bayyana cewar har yanzu tattalin arzikin duniya na fuskantar mawuyacin hali da suka hada da rashin habbaka kamar yadda ya dace, ga faduwar kasuwanni, da kuma banbancin yarjeniyoyin kasuwancin da kasashen suka kulla.
Shugaban ya bayyana fatar ganin wanan taron ya gabatar da hanyoyin da za’a bunkasa tattalin arzikin duniya da kuma inganta shi kamar yadda yake a baya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu