Obama ya bukaci Amurkawa su hada kai
A yayin da Amurka ke bikin tunawa da mutanen da suka rasu a harin ranar 11 ga watan Satumba, shugaba Barack Obama ya bukaci al'ummar kasar da su hada kansu don ganin 'yan ta'adda ba su raba kan kasar ba.
Wallafawa ranar:
Obama ya ce, babu wata kalma da za ta share radadin rashin jama'ar da aka yi a harin wanda aka kaddamar shekaru 15 da suka gabata, amma ya bukaci Amurkawan da su tsaya kai da fata don ganin cewa kungiyoyi irin na IS da al-Qaeda ba su kawo rarrabuwar kawuna a kasar ba.
Kusan mutane dubu 3 ne suka rasa rayukansu a farmakin na wancan lokacin wanda al Qaeda ta kaddamar a New York da Washington.
Hilary Clinton ta Democrat da Donald Trump na Republican duk sun dakatar da yakin neman zabensu don halartar bikin tunawa da wannan rana.
Sai dai a yayin gudanar da bikin, Mrs. Clinton ta gamu da rashin lafiya saboda tsananin zafi da aka yi a taron.
Rahotanni sun ce, Clinton ta samu sauki bayan da ta samu hutu a gidan 'yarta da ke New York.
Abokin hamayyarta Donald Trump, ya tambayi halin rashin lafiyar da ta tsinci kanta a ciki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu