Isa ga babban shafi
Amurka

Clinton da Trump za su tafka muhawara a yau

Yau ne 'yan takaran shugabancin Amurka Hillary Clinton da Donald Trump za su tafka muhawararsu ta farko a kafar talabijin, in da za su bayyana wa Amurkawa manufofin da suka tanada don inganta rayuwarsu. 

Hillary Clinton da Donald Trump
Hillary Clinton da Donald Trump REUTERS/Lucy Nicholson (L) and Jim Urquhart/File Photos
Talla

Akalla mutane miliyan 90 ake saran za su kalli mahawarar ta akwatin talabijin, wadda kuma za ta bude kofar janyo hankalin masu kada kuri’ar da har yanzu, ba su yanke shawara kan wanda za su zaba ba.

Rahotanni na nuna cewar, Clinton ta jam'iyyar Democrat da Trump na Republican na ci gaba da tafiya kai da kai a kuri’un jin ra’ayoyin jama’a.

Za a dai tafka muhawarar  ce da misalin karfe 9 na dare agogon kasar, wanda ya yi dai dai da karfe 1 na tsakiyar dare agogon GMT, wato a gobe talata kenan.

Ana saran gudanar da zaben shugabancin kasar ta Amurka a ranar 8 ga watan Nuwamba mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.