rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Majalisar Dinkin Duniya Portugal

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Guterres ya zama sakatare janar na MDD

media
Sabon sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antônio Guterres REUTERS/Denis Balibouse/File photo

Tsohon Firaministan kasar Portigal Antonio Guterres, na gab da darewa kan mukamin babban magatakarda na Majalisar Dinkin Duniya bayan da a yau kasashe 15 mambobi a kwamitin tsaro na Majalisar sun jefa kuri’a zagaye na shida da ke tabbatar da cewa ya fi sauran ‘yan takara samun kuri’u.


Jim kadan bayan jefa kuri’ar a wannan laraba, jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Vitaly Churkin, ya ce ba wata tantama Guterres ne zai dare kan wannan mukami.

Mr. Guterres mai shekaru 67, shi ne wanda ya jagoranci hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya na tsawon shekaru 10.

A ranar 1 ga watan Janairun badi ne, sabon magatakardan zai fara aiki bayan Ban Ki Moon ya sauka.