Isa ga babban shafi
Syria

Rasha za ta jibge dakaru a Syria

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya tabbatar da yarjejeniyar da suka kulla da gwamnatin Bashar Al Assad da za ta ba Moscow damar tura dakarunta zuwa Syria. Wannan wani mataki ne da ake ganin Dakarun Rasha za su ci gaba da kasancewa a Syria a lokaci mai tsawo.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin Ivan Sekretarev/Reuters
Talla

Shugaba Putin ya amince da dokar ne da za ta ba Rasha damar kafa sansanonin soji da na jiragen yaki a Syria domin ci gaba da taimakawa dakarun Bashar Al Assad.

A watan Agustan 2015 ne gwamnatin Rasha da Syria suka sanya hannu kan yarjejeniyar, kuma a yau Jum’a ne Shugaba Putin ya tabbatar da dokar bayan majalisar kasar ta kada kuri’ar amincewa da matakin.

Dokar dai ta ba dakarun Rasha kariya ne a Syria, kuma ana ganin za su ci gaba da zama a kasar domin taimakawa dakarun gwamnatin Assad yakar ‘yan tawaye.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da Rasha ke ci gaba da fuskantar suka da tir da allawadai daga manyan kasashen yammaci kan hare haren sama da jiragenta ke kai a gabacin Aleppo.

Kimanin dakarun Rasha 4,000 aka bayyana cewa suna cikin Syria yanzu haka tare da jiragen yaki da dama.

Amurka dai na zargin Rasha da aikata laifukan yaki a Aleppo, a yayin da a gobe asabar ake sa ran sakataen harakokin wajen Amurka John Kerry zai gana da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov kan batun tsagaita wuta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.