Isa ga babban shafi
Myanmar

Mutane Akalla 30 Sun Mutu A Sabon Tarzoma A Myanmar

A kasar Myanmar mutane da yawa ne suka rasa rayukansu a wani sabon rikici daya barke a jihar Rakhine inda aka yi ta samun tarzoma a baya, inda yanzu mutane sama da 30 suka gamu da ajalin su.

Jagoran gwagwarmaya na kasar Myanmar kuma Ministan Waje na kasar  Aung San Suu Kyi
Jagoran gwagwarmaya na kasar Myanmar kuma Ministan Waje na kasar Aung San Suu Kyi rfi
Talla

Majiyoyin Soja a yankin sun bayyana cewa an kwace kwanaki biyu ana tarzoman kuma akwai alamun rikicin bai lafa ba.

Jihar Rakhine nan ne mazaunin musulmi marasa yawa na Rohingya wadda take kan iyaka da kasar Bangladesh.

Sojan kasar Myanmar na tsare da wannan yanki kuma sau da yawa akan kai samame domin koda a watan jiya saida aka kasha ‘yan sanda tara a yankin.

Sojoji sun kashe mutane da dama yayin da suke farautar mutanen da suka kashe masu ‘yan uwa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.