Isa ga babban shafi
Brazil

Jirgin sama dauke da ‘Yan wasan Brazil ya fadi a Colombia

Wani jirgin sama dauke da ‘yan wasan wata kungiya kwallon kafa ta Brazil ya fadi a kusa da garin Medellin na Colombia dauke da mutane 72 bayan ya fito daga Bolivia.

Jirgin sama ya fadi da 'Yan wasan Chapecoense ta Brazil a Colombia
Jirgin sama ya fadi da 'Yan wasan Chapecoense ta Brazil a Colombia REUTERS/Paulo Whitaker
Talla

Rahotanni sun ce jirgin mai lamba CP2933 na dauke ne da yan wasan kungiyar Real Chapecoense. Hukumomin filin jirgin Medellin sun ce akwai mutane 6 da suka rayu a hatsarin jirgin.

Magajin garin Madellin ya ce alamu ya nuna mai ne ya kare a jirgin.

‘Yan wasan kungiyar Chapecoense Real na kan hanya ne domin buga wasa da Atletico Nacional ta Colombia a ranar Laraba.

Ya zuwa yanzu dai babu cikkaken bayani kan makomar yan wasan da ke cikin jirgin da kuma masu horar da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.