rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Daular Larabawa Faransa Al'adu UNESCO Majalisar Dinkin Duniya Iraqi Syria

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An kafa asusun kare kayayyakin tarihi a duniya

media
shugaban kasar Faransa Francois Hollande a wajen taron kare kayan tarihi a Abou Dhabi. Reuters

Wakilan kasashen duniya 40 sun amince da shirin kafa wani asusu da zai taimaka wajen kare cibiyoyi da kuma kayayyakin tarihi da ke fuskantar barazana a kasashen da ke fama da yaki.
 


Wakilan sun amince da haka ne a yayin rufe wani taron kwanaki biyu da suka gudanar a birnin Abu Dhabi na Hadaddiyar Daular Larabawa.

To sai dai taron bai sanar da kayyadaden kudin da za a zuba a asusun ba, yayin da shugaban Faransa Francois Hollande da ke cikin mahalarta taron, ya bayyana cewa, mai yiwuwa asususn ya samu Dala miliyan 100.

Kasar Faransa ce ta bayar da shawarar gudanar da taron ta re da hadin gwiwar hukumar kula da ilimi, kimiya da kuma tattalin al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO, lura da yadda ake ci gaba da lalata kayan tarihi a kasashen da ke fama da yake-yake duniya da suka hada da Syria da Iraqi, in da mayakan IS ke ikirarin jihadi.