rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

UNESCO Syria Iraqi Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Taron duniya domin kare kayayyakin tarihi a Abu Dhabi

media
Hollande a gidan ajiye kayayyakin tarihi na Louvre DR

Wakilan kasashen duniya 40 ne ke halartar wani taro da nufin samar da wani asusu da zai taimaka wajen kare cibiyoyi da kuma kayayyakin tarihi da ke fuskantar barazana musamman a kasashen da ke fama da tashe-tashen hankula.


Taron wanda ke gudana a birnin Abu Dhabi na Haddadiyar Daular Laranawa, Faransa ce ta bayar da shawarar gudanar da shi ta re da hadin gwiwar Hukumar kula da ilimi, kimiya da kuma tattalin al’adu ta MDD wato UNESCO lura da yadda ake ci gaba da lalata kayan tarihi a kasashen da ke fama da yake-yakea duniya.

Shugaban Faransa Francois Hollande daya daga cikin mahalarta taron, zai yi amfani da wannan dama domin ziyartar sabon gidan ajiye kayayyakin tarihi na Louvre da ke Abou Dhabi, wadda ake shirin budewa a cikin shekara ta 2017.