Isa ga babban shafi
Syria

Syria ta ki amince wa da tsagaita wuta a Aleppo

Gwamnatin Syria ta bayyana cewa, ba za ta amince da yarjejeniyar tsagaita musayar wuta a birnin Aleppo ba, har sai ta samu tabbacin ficewar ‘yan tawaye daga birnin. 

Fararen hula na cikin wani hali a gabashin birnin Aleppo na Syria
Fararen hula na cikin wani hali a gabashin birnin Aleppo na Syria AMEER ALHALBI / AFP
Talla

Kamfanin dillancin labarai na SANA ya rawaito ma’aikatar harkokin wajen Syria na cewa, gwamnatin ba za ta yi sakaci har ‘yan ta’adda su yi garkuwa da fararen hula a gabashin birnin Aleppo ba, yayin da ta lashi takobin daukan matakan da suka dace na ceto su.

Wannan dai shi ne da dalilin da ya tinzira gwamnatin har ta yi watsi da duk wani yunkuri na cimma yarjejeniyar tsagaita musayar wuta wadda ba ta kunshi ficewar ‘yan ta’adda daga birnin na Aleppo ba.

Tun lokacin da suka kaddamar da farmakin kwace birnin makwanni uku da suka gabata, dakarun Syria sun yi nasarar karbe kashi biyu bisa uku na birnin, wanda a can baya ya kasance karkashin ikon ‘yan ta’addan.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, kasar Syria ta yaba da matakin da Rasha da China suka dauka na yin watsi da kudirin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ya bukaci cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki bakwai a Aleppo.

A karo na shida kenan da Rasha ta yi watsi da irin wannan kudirin, yayin da sau biyar kenan da itama China ta yi haka.

Syria na ganin dai, kudirin zai bai wa ‘yan ta’adda damar sake kintsawa don ci gaba da kai hare-hare nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.