rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Congo Brazaville Libya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Babu zancen ganawa tsakanin Trump da Nguesso

media
Shugaban Amurka mai jiran gado, Donald Trump 路透社

Wata majiya a kusa da shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump, ta musanta bayanan da ke cewa an tsara wata ganawa tsakaninsa da shugaban kasar Congo Brazzaville Denis Sassou Nguesso.


Kamfanin dillancin Amurka Reuters, ya jiyo wata babbar jami’a ta kusa da shugaba Trump na cewa, a cikin abubuwan da aka tsara shugaban mai jiran gado zai yi a ranar Talata, ba batun ganawa da shugaban Congo.

Fadar shugaban na Congo ta sanar a ranar Litnin cewa, Sassou Nguesso zai gana da Donald Trump domin tattaunawa kan batutuwa da dama ciki har da rikicin Libya.