Isa ga babban shafi

Amurka ta kori Jami’an Rasha 35

Gwamnatin Amurka ta kori jami’an diflomasiyar Rasha guda 35 tare da kakaba takunkumi ga wasu hukumomin leken asiri guda biyu a wani mataki na mayar da martani ga zargin shiga sha’anin zaben kasar da aka gudanar a watan jiya.

Shugaban Rasha Vladimir Putin, da  Barack Obama na Amurka
Shugaban Rasha Vladimir Putin, da Barack Obama na Amurka ALEXEI DRUZHININ / SPUTNIK / AFP
Talla

Gwamnatin Obama na zargin gwamnatin Putin na Rasha da yin kazalandan ga harakokin zaben Amurka da aka gudanar a watan Nuwamba domin marawa Donald Trump baya na Jam’iyyar Republican da ke jiran gado yanzu haka.

Jami’an leken Asirin Amurka sun yi amannar cewa Rasha ta yi kutse ga jam’iyyar Democrat da sakwannin Imel na ‘yar takarar jam’iyyar Hillary Clinton.

Shugaba Obama ya fadi a cikin wata sanarwa cewa korar jami’an martani ne akan Rasha ga kotsen da ta yi a zaben Amurka.

Jami’an Rasha 35 ne Amurka ta kora tare da kakabawa wasu hukumomin leken asirin Rasha guda biyu takunkumi. Sannan akwai wasu gidajen Rasha biyu da Amurka ta sa aka rufe.

Sai dai kuma shugaba Donald Trump mai jiran gado ya ce zai gana da manyan jami’an leken asirin Amurka a mako mai zuwa domin yi ma shi bayani akan zargin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.