Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya soki Merkel akan karbar Baki

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya ce shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi babban kuskure na amincewa da karbar baki ‘Yan gudun hijira da ‘Yan ci-rani miliyan guda.

Shugaban kasar Amurka mai jiran gado Donald Trump ya soki kungiyar tsaro ta NATO
Shugaban kasar Amurka mai jiran gado Donald Trump ya soki kungiyar tsaro ta NATO REUTERS/Mike Segar
Talla

“Babban kuskure ne ta amince da ‘Yan gudun hijirar da ba ta san inda suka fito ba” a cewar Trump.

Trump wanda ya rage kwanaki hudu a rantsar da shi ya yi wannan furucin ne game da Jamus a tattaunawar shi da Jaridar Times ta Birtaniya da kuma Bild ta Jamus.

A tattaunawar Trump ya ce kungiyar tsaro ta NATO ba ta da wani amfani, tare da cewa zai iya kulla yarjejeniya da Rasha da sassauta takunkuman da Amurka ta kakaba ma ta.

Sannan Trump ya yaba da ficewar Birtaniya a Tarayyar Turai tare da bayyana fatar kulla kawance mai karfi da ita bayan ta fice.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.