Isa ga babban shafi
Mexico

Mexico ta ba Amurka El Chapo

Gwamnatin Mexico ta mika wa Amurka babban shugaban masu fataucin miyagun kwayoyi Joaquin da ake kira El Chapo Guzman domin fuskantar shari’a a kasar.

El Chapo babban shugaban masu fataucin miyagun kwayoyi a Mexico
El Chapo babban shugaban masu fataucin miyagun kwayoyi a Mexico REUTERS/Tomas Bravo/File Photo
Talla

Ana tuhumar Guzman da laifukan fataucin miyagun kwayoyi zuwa Amurka da gwamnatin Mexico ta dade tana kokarin magancewa.

Guzman ya isa New York, inda zai iya fuskantar hukuncin daurin rai da rai a gidan yarin Amurka.

Sau biyu Guzman na haka rame ta karkashin kasa yana sulalewa a gidan yari. A yau Juma’a ake sa ran zai gurfana gaban kotun Amurka a Brooklyn.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.