rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Syria Rasha Iran Majalisar Dinkin Duniya Kazakhstan

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Za mu ci gaba da yaki a Syria- 'Yan tawaye

media
Zaman tattaunawar sulhu tsakanin 'yan tawayen Syria da gwamnatin kasar a birnin Astana na Kazakhstan Reuters/Mukhtar Kholdorbekov

‘Yan tawayen Syria sun lashi takobin ci gaba da yaki matukar tattaunawar sulhu tsakaninsu da gwamnatin kasar ta sukurkuce.


Bangarorin biyu sun tashi baram-baram a zaman da suka fara a yau a birnin Astana na Kazakhstan ba tare da cimma wata matsaya ba.

Dukkanin bangarorin biyu sun tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP da rashin cimma matsaya a tsakaninsu.

An dai yi fatan wannan tattaunawar ta zamanto irinta ta farko da bangarorin biyu ke zaman keke da keke da nufin kawo karshen rikcin kusan shekaru shida da ya yi sanadiyar ajalin dubban mutane.

To sai dai ‘yan tawayen sun janye daga tattaunawar saboda yadda dakarun Syria ke ci gaba da lugudan wuta tare da kai hare-hare a kusa da birnin Damascus.

A gobe Talata ne ake saran ci gaba da zaman sulhun wanda kasashen Rasha ta Turkiya da Iran suka shirya a birnin Astana.

Ana dai fatan wannan tattaunawar ta zama tamkar sharen fage ga zaman sulhun da Majalisar Dinkin Duniya za ta jagoranta tsakanin bangarorin biyu a birnin Geneva a cikin wata mai zuwa.