Isa ga babban shafi
Syria

Rasha ta Turkiya na son tabbatar da tsagaita buda wuta a Syria

Kasashe Rasha da Iran da Turkiya da ke jagorantar sasanta rikicin Syria a Kazakhstan sun amince a tsagaita buda wuta a fadin Syria. Amma har yanzu babu wani matakin siyasa da aka dauka na warware rikicin kasar bayan kwana biyu ana tattaunawa tsakanin wakilan gwamnatin Assad da ‘Yan tawaye a Astana

Tawagar Yan tawayen Syria da Mohamed Allouche ke jagoranta a taron Astana
Tawagar Yan tawayen Syria da Mohamed Allouche ke jagoranta a taron Astana REUTERS/Mukhtar Kholdorbekov
Talla

Jekadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman a rikicin Syria Steffan de Mistura, ya ce za su yi kokarin tabbatar da ingancin yarjejeniyar tsagaita buda wutar tsakanin bangarorin biyu.

A cewar De Mistura amincewa da tsagaita buda wuta ne zai taimaka a ci gaba da tattauna hanyoyin warware rikicin Syria.

Sai dai babu tabbas ko bangarorin da ke rikici a Syria za su amince da matakin da kasashen uku suka amince.

Rikicin Syria dai ya lakume rayukan mutane sama da dubu 300 tare da raba miliyoyan ‘Yan kasar da gidajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.