rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Malaysia China

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Wani jirgin ruwa dauke da mutane 31 yawanci 'yan kasar China ya bace a tekun Malaysia

media
Wani jirgin ruwa na Malaysia da yayi dawainiya wajen neman wani jirgin saman kasar da ya fada cikin teku kwanan baya REUTERS/Australian Defence Force/Handout via Reuters

Wani jirgin ruwa dauke da masu yawon shakatawa ciki har da ‘yan kasar China 28 ya bace a yankin tekun kasar Malaysia.


Majiyoyin samun labarai sun fadawa kamfanin Dillancin Labaran Faransa, AFP cewa mutane 31 ke cikin jirgin kuma tun jiya Asabar aka daina jin duriyar jirgin ruwan.

Bayanan na nuna ana chan ana ci gaba da bincike domin samin takamaiman abinda ya faru.