Amurka ta soki Rasha saboda Ukraine
Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley ta yi mummunar suka kan matakan da Rasha ke dauka kan Ukraine, in da ta yi alkawarin cewar Amurka za ta taimaka wa gwamnatin kasar.
Wallafawa ranar:
A jawabin ta na farko ga kwamitin Sulhu na Majalisar, Haley ta ce ba za a cire wa Rasha takunkumin da aka kakaba mata a shekrar 2014 saboda mamayar da ta yi wa Crimea ba, har sai ta mayar wa Ukraine yankin.
Haley ta ce Amurka na bukatar sabuwar dangantaka da Rasha amma halin da ake ciki a Ukraine ya zama dole su dauki mataki akai.
Shugaban Amurka Donald Trump ya nuna alamar karfafa dangantaka da gwamnatin Vladimir Putin ta Rasha.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu