rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Cutar Sida Lafiya Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Bada kulawa zuwa mutanen da suka kamu da cutar Sida a Duniya

media
Gwajin sabon rigakafin Sida ko Aids AFP PHOTO/RODGER BOSCH

Wasu kungiyoyi dake kare hakkokin marasa lafiya da suka kamu da cutar kanjamau ko Sida (PILS ) sun gudanar da wani taro a zauren majalisar dattijan kasar Faransa, sun kuma shigar da kira zuwa hukumomin kasashe na su mayar da hankali tareda bada kulawa da ta dace domin kare mutanen da suka kamu da wannan cuta.


Rahoto daga kungiyoyin ya gaskanta wasu sakamakon bincike da suka gudanar a kasashe, binciken dake nuna ta yada mutanen da suka kamu da wannan cuta ke fuskantar muzgunawa dama rashin kulawa da ta dace daga hukuma dama sauren jama'a.
Cutar na kashe akala mutane 3000 a kowace rana yayinda wasu kasashen ke fuskantar karanci  ko rashin isasun kayyakin kariya domin kulawa da mutanen da suka kamu da cutar .