Korea ta Arewa ta sake gwajin makami mai linzami
Korea ta Arewa ta sake gwajin makami mai linzami da safiyar yau Lahadi wanda ke kasancewa karon farko tun bayan da shugaba Amurka Donald Trump ya dare karagar mulki.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Hukumomin Korea ta Kudu mai makwabtaka da ita ne suka tabbatar da hakan, inda suka ce makamin da aka harba ya yi nisan zangon kilomita dari biyar kuma ya nufi Tekun Japan.
A wata ganawa da shugaban Amurka Donald Trump, Firaministan Japan Shinzo Abe, ya ce ba za a amince da wannan hallayar ta Korea ta Arewa ba, inda shugaba Trump ya ba shi tabbacin goyon baya.
Korea ta Arewa dai ta gwada makamai masu linzami da kuma nukiliya da dama a shekarar da ta gabata duk da gargadi Majalisar Dinkin Duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu