rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Pakistan Indonesia Malaysia Kungiyar kasashen Asiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Wasu kasashen duniya sun haramta Valentine

media
Wasu kasashen Musulmi na adawa da bukukuwan Valentine REUTERS/Omar Sanadiki

Yau ranar 14 ga watan Fabarairu rana ce da ake yiwa lakabi da ranar masoya ta duniya, wato Valentine, wanda aka fara gudanar da bukukuwa tun shekaru 259 da suka gabata.


Kasashe irin su Australia da Malaysia da Singapore sun gargadi matasa da suyi taka tsan-tsan musamman ganin yadda soyayar da ake ta kafar sada zumunta ke haifar da matsala.

Kasashe kuma irin su Paksitan da Indonesia sun haramta bikin da suka bayyana a matsayin al'adar yahudawa ta koyar da ayyukan lalata.

A kasar Japan an gudanar da zanga-zanga dan ganin an haramta yadda matasa maza da mata ke mu’amala a bainar jama’a.