Isa ga babban shafi
G20

Taron G20 zai nemi sanin manufofin Trump

Ministocin kungiyar kasashe 20 da suka fi habakar tattalin arzikin duniya da ake kira G20 za su fara taro a birnin Bonn na kasar Jamus inda za su mayar da hankali ga neman sanin Manufofin Trump a ganawar farko da za su yi da sabon sakataren harakokin wajen kasar Rex Tillerson.

Ministocin kungiyar kasashe 20 da suka fi habakar tattalin arzikin duniya da ake kira G20 za su fara taro a birnin Bonn na kasar Jamus
Ministocin kungiyar kasashe 20 da suka fi habakar tattalin arzikin duniya da ake kira G20 za su fara taro a birnin Bonn na kasar Jamus REUTERS
Talla

Taron zai ba Sabon Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson damar yi wa takwarorinsa bayani kan taken Trump na Amurka Farko da gwamnatin shi ke yayatawa.

Ministocin Turai za su nemi yadda manufar Trump za ta shafi huldar Amurka da kasashen duniya.

Sauran batutuwan da taron zai mayar da hankali sun hada da rikicin kasar Ukraine da harkokin kasuwancin China da rikicin Syria da Gabas ta Tsakiya, sai kuma makomar kungiyoyin NATO da kungiyar kasashen Turai.

Karfin tattalin arzikin Kasashen G20 ya kunshi kashi 85 na tattalin arzikin duniya, kashi biyu bisa uku na yawan jama’a..

Taron ministocin share fage ne ga taron shugabannin kungiyar G20 da za a gudanar a watan Yuli a Hamburg inda shugaban Amurka Donald Trump zai hadu da takwaransa na Rasha Vladimir Putin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.