rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Korea ta Arewa Malaysia Diflomasiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Korea ta Arewa ta zargi Malaysia da kashe dan’uwan Kim Jong-Un

media
Kim Jong Nam dan uwan shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un Joongang Ilbo/News1 via REUTERS

Huldar Diflomasiya tsakanin Korea ta Arewa da Malaysia na neman sukurkucewa kan kisan dan uwan shugaba Kim Jong-Un, wato Jong-Nam.


Wannan na zuwa ne yayin da masu bincike ke ci gaba da nazarin hotunan bidiyon da ke nuna yadda aka kai wa Jong-Nam hari a filin jiragen Kuala Lumpur.

A halin yanzu Korea ta Arewa ta janye jakadanta daga Malaysia inda take masa tambayoyi kan wannan kisa.

Kasar ta ce yanzu kwananki 7 kenan da aikata wannan kisa, sai dai babu gamsasun shaidu kan dalilin mutuwar Kim Jong-Nam, kuma korea ta ce bazata iya amincewa da binciken ‘yan sanda Malaysia ba.

Fadar shugaban korea ta Arewa ta kuma soki binciken gawar da aka gudanar ba tare da neman izinin su ba, korafin da Malaysia ta ce bashi da wata ma’ana.

Ma’aikatar harkokin kasashen wajen Malaysia, ta ce tunda mutuwar ya faruwa ne a kasarta, ita ke da hakkin gudanar da cikakken binciken makasudin mutuwar domin gano ainihi abin da ya faru.

Friministan Malaysia Najib Razak ya ce kasar ba za ta yi abin da zai bata kimar ta a idon duniya ba, kuma yana da tabbacin za a gudanar da binciken a cikin kwarewa.

Hotunan bidiyon farko da aka fitar kan kisan Jong-Nam ya nuna wasu mata biyu sun doshi inda yake tare da rufe masa fuska da kyale.