rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Myanmar Antonio Guterres

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa kan halin da yan kabilar Rohinga suke ciki

media
'Yan gudun hijira daga kabilar Rohingya Musulmi daga Myanmar

Manzon Majalisar Dinkin Duniya  ya isa kudancin kasar Bangladesh domin ganawa da ‘yan gudun hijirar Rohinga da suka tserewa kisan kiyashi daga kasar Myanmar.

A yan kwanuki da suka gabata Majalisar dinkin duniya ta ce tawagarta ta masu bincike kan tauye hakkin dan’adam, zata fara gudanar da bincike kan zargin cin zarafin Musulmi ‘yan kabilar Rohingya a kasar Myanmar.


Yanghee Lee, na ziyara ne a wasu sansanonin da ke kunshe da ‘yan gudun hijira dubu 73, wadanda suka tsere bayan da sojoji da ‘yan sanda suka afka wa wasu kauyukan kasar ta Myanmar.