Isa ga babban shafi
UNICEF

Sama da yara miliyan daya na iya rasa rayukansu cikin 2017 - UNICEF

Majalisar Dinkin Duniya tayi gargadin cewar yara kanana kusan miliyan daya da rabi ne ke fuskantar barazanar mutuwa saboda rashin abinci mai gina jiki a wasu kasashe 4 na duniya cikin wannan shekara ta 2017.

Wasu kananan yara a sansanin 'yan gudun hijira da ke birnin Sana'a a kasar Yemen
Wasu kananan yara a sansanin 'yan gudun hijira da ke birnin Sana'a a kasar Yemen financialtribune.com
Talla

Daraktan hukumar UNICEF Anthony Lake, ya bukaci tallafin gaggawa dan ceto wadannan yara daga hadarin da suke fuskanta.

Kididigar da hukumar ta bayar ya nuna cewa a kasar Yemen, inda aka kwashe shekaru biyu ana gwabza yaki, yara 462,000 ke fama da rashin abinci mai gina jiki, yayin da Najeriya ke da yara 450,000 dake fuskantar wannan matsala a Yankin Arewa maso gabashin kasar, saboda rikicin Boko Haram.

Wata kungiyar mai suna Fews Net, da itama ta yi gargadi kan halin da ake ciki, tace tun a bara wasu yankunan jihar Barno ke fama da yunwar saboda yadda kungiyoyin agaji suka kasa isa yankunan da suka kamata.

UNICEF ta kuma ce, farin da aka samu a kasar Somalia ya jefa yara 185,000 cikin mummunan yanayi, kuma adadin na iya karuwa zuwa 270,000.

Hukumar tace a Sudan ta kudu inda akayi shelar yunwa, yara 270,000 ke fama da yunwa a Jihar Unity kadai.

Ana saran wakilan kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, su ziyarci arewacin Najeriya, Kamaru, Chadi da kuma Nijar a watan gobe, dan janyo hankalin duniya kan yadda al’amura suka tabarbare a yankunan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.