rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Malaysia Korea ta Arewa Saudiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Malaysia ta ce filin jiragen sama na Kuala lumpur ba bu hatsari.

media
Hoto na Kyamaran filin jirgin saman Kuala Lumpur wanda ya nuna mutumin da ake zargi an kashe 路透社

Hukumomi a kasar Malaysia sun bada tabbacin cewa filin sauka da tashin jiragen sama na kasar dake Kuala Lumpur na cikin yanayi mai kyau, kuma babu wani abin fargaba bayan kisan da aka yiwa wani dan uwan shugaban Korea ta Arewa  inda aka yi amfani da wani shu'umin guba makon jiya.

 


Ranar 13 ga wannan wata ne dai Kim Jong Nam dan uwan shugaban Korea ta Arewa ya  mutu bayan da aka fesa masa wani guba.

Jami'in ‘Yan Sanda Abdul Samat Mat wanda yake binciken kisan ya fadawa manema labarai cewa an tabbatar babu sauran guggubin irin wancan guba a harabar filin jirgin saman na Kuala Lumpur.

Wasu kafofin labarai sun nuna hoton Video na kyamaran da aka dasa a filin jirgin saman dake nuna wasu mata biyu da ake zargi da hannu wajen kisan mutumin.

A halin da ake ciki Sarki Salman na kasar Saudiya na ziyara a Malaysia yau domin kara dankon zumunci tsakanin kasar Saudiya da Malaysia.