Isa ga babban shafi
Amurka

'Yan Democrat na matsin lamba ga Sessions na Amurka

‘Yan Jam’iyyar Democrat na Amurka na ci gaba da caccakar babban mai shari’a na kasar Jeff Sessions, in da suka ce ba su gamsu da bayanansa ba game da ganawarsa da jakadan Rasha a bara. 

Jeff Sessions na Amurka na fuskantar matsin lamba daga bangaren jam'iyyar adawa ta Democrat
Jeff Sessions na Amurka na fuskantar matsin lamba daga bangaren jam'iyyar adawa ta Democrat REUTERS/Kevin Lamarque/File Photo
Talla

Shugabar ‘yan Democrat a majalisar wakilan kasar Nancy Pelosi ta jaddada bukatar ganin Sessions ya sauka daga mukaminsa.

Sai dai shugaban Amurka Donald Trump ya ce, babban mai shari’ar mutumin kirki ne yayin da ya bayyana matsin lambar da ake yi masa a mtsayin bita da kulli.

Mr. Sessions dai ya tsame kansa a game da binciken hukumar FBI kan wannan zargin na ganawa da jakadan Rasha da nufin kutse a zaben shugabancin kasar da aka gudanar a bara.

Sannan ya ce, babu wata karya da ya yi a gaban Majalisar Dattawa a yayin tabbatar da shi a matsayin babban mai shari'a, in da ya musanta zantawa da Rashawa.

Sessions dai ya taka muhimmiyar rawa a yakin neman zaben shugaba Donald Trump.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.