rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Jordan Kungiyar Kasashen Larabawa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An aiwatar da hukuncin kisan mutane 15 a kasar Jordan

media
Sarki Abdallah na biyu na kasar Jordan yana jawabi ga MDD REUTERS/Ray Stubblebine

Hukumomi a kasar Jordan yau Asabar  suka aiwatar da hukuncin kashe wasu mutane 15 da ake zargi sun aikata lafuka barkatai tsakanin shekara ta 2006 da shekara ta 2014.

 


Ministan labarai na kasar ta Jordan Mahmud al-Momani ya tabbatar da cewa tuni mutanen na lahira kuma dukkanin su ‘yan kasar ta Jordan ne.

A cewar sa 10 daga ciki an zarge su ne da laifin ayyukan ta'addanci, yayinda biyar an zarge su ne da laifukan da suka hada da fyade.

A gidan yarin birnin Amman ne , inji Ministan aka rataye su duka.