rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Malaysia Korea ta Arewa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Malaysia ta kori jekadan Koriya ta Arewa

media
Koriya ta Kudu ta zargi Koriya ta arewa da kisan Kim-Jong-nam TOSHIFUMI KITAMURA / AFP

Malaysia ta kori jekadan Koriya ta Arewa kan kisan Kim Jong Nam dan uwa ga shugaban kasar ta koriya ta Arewa Kim Jong-un Ma’aikatar harakokin wajen Malysia ta ba jekadan kasar sa’o’i 24 ya fice daga kasar.


Kim Jong-Nam wanda suke uba guda da shugaban Koriya ta arewa an kashe shi ne a makwanni uku da suka gabata bayan wasu mata biyu sun barbada masa sinadari mai guba a fuska a tashar jirgin sama a Kuala Lumpur.

Kisan dai ya dada lalata dangantakar diflomasiya tsakanin Malaysia da Koriya ta Arewa inda hukumomin Kuala Lumfur suka ki mika gawar Jong-Nam ga gwamnatin Pyongyang.

Koriya ta Kudu ta fito ta zargi gwamnatin Koriya ta arewa da hannu ga aikata kisan.